Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin ‘Yan Najeriya Kan Rufe Wasu Makarantu Bayan Sace Dalibai a Katsina


Kwanaki 5 bayan sace wasu daliban makarantar sakandare da ‘yan bindiga su ka yi a garin Kankara da ke jihar Katsina, wasu jihohin arewacin Najeriya sun dauki matakin rufe makarantunsu. Sai dai jama’a da sauran masana harkokin ilimi na ganin wannan tamkar bada kai ne ga ‘yan ta’adda a kasar.

A yayin da yanzu haka ake ci gaba da bibiyar inda aka shigar da daliban na makarantar kimiya da fasaha ta Kankara a jihar Katsina bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace su, wasu jihohin arewacin kasar da ke makwabtaka da jihar Katsina da ita kanta jihar ta katsina sun rufe makarantun jihohin nasu a matsayin matakin riga kafi.

Bayan jihar Katsina, jihar Zamfara ita ma ta rufe wasu makaratu da ke kusa da kan iyakar jihar da Katsina. Haka zalika an rufe makarantun a jihohin Kaduna, Kano da Jigawa a matsayin matakin kariyar dakile yaduwar cutar COVID-19, a cewar hukumomin jihohin.

Wasu ‘yan Najeriya na ganin matakan da gwamnatocin suka dauka na tsaro akan makarantu sun dace, wasu kuwa na ganin tamkar bada kai ne bori ya hau ga kungiyoyin da ke adawa da makarantun boko a kasar, kuma wannan ba shi ne karon farko da aka sace yara a makarantun boko a arewacin Najeriya ba.

Chairman Ado Shu'aibu Dansudu, wani mazaunin garin Legas, ya ce gaskiya matakin bai dace ba kuma tamkar ana lallaba ‘yan ta’adar ne, hakan na nuna su ne su ke yin nasara.

Muhammad Sani, Malamin makaranta ne, ya ce ya na ganin matakin na gwamnati gazawa ne daga bangarenta, kuma arewacin Najeriya da ake fama da rashin masu zuwa makaranta zai karu kenan, don haka ya kamata gwamnatocin wadannan jihohi su sake tunani.

Yanzu haka dai ana ci gaba da samun kiraye-kiraye daga hukumomin duniya da masu fada a ji akan ganin an hanzarta sako daliban da aka sace ba tare da bata lokaci ba. Sai dai ganin yadda har yanzu gwamnati ba ta samu nasarar gano wasu daliban da aka sace a can baya ba kamar ‘yan makarantar Chibok da Dapci, hakan ya sa a wannan karon wasu ke fargaban abinda ka je ya dawo.

XS
SM
MD
LG