Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Nuna Shakku Kan Shirin Daukan Malamai 3000 a Taraba


Gwamna Darius Dickson Ishaku Na Jihar Taraba.
Gwamna Darius Dickson Ishaku Na Jihar Taraba.

Shirin daukar malamai 3000 aiki na tsawon wa’adin shekaru biyu ana biyansu albashin Naira 30,000 ga masu digiri, da kuma Naira 20,000 ga masu NCE da gwamnatin jihar Taraba ta kuduri aniyar yi ya gamu da shakku, ganin cewa tana fuskantar matsalar biyan albashi a jihar.

Shugaban kungiyar raya Jukunawa ta kasa Mista Bako Benjamin, ya fada a hirarsa da Muryar Amurka cewa suna da shakku kan yadda gwamnatin dake kokawa da rashin kudin biyan albashin ma’aikata da take da su a halin yanzu za ta sake daukar dawainiyar karin albashin mutane 3000.

Da yake kare matsayin gwamnati, kwamishinan ilimi na jihar Taraba Mista Johanes Jigem, ya ce rukuni na malaman da za su dauka za su karantar a makarantun gaba da firamare ne kawai.

Ya kuma kara da cewa babu ma’aikacin gwamnatin jiha dake bin ta bashi na albashi illa ‘yan matsaloli da ake fama da su wajen warware batun albashin malaman firamare.

Dangane da batun daidaita biyan albashin ma’aikata a jihar ta Taraba, duk da tallafin da ta samu daga asusun gwamnatin Tarayya da kuma matakan dakile wawurar kudin da gwamnati ke zargin manyan ma’aikata da aiwatarwa da ta ke dauka, kwamishinan yada labarai Barr. Anthony Danburam, ya ce gwamnati ta gano akwai zagon kasa da ake kulla mata kuma a shirye ta ke ta magance hakan.

Domin jin karin bayani saurari rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG