Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yiwa Shugabanni Addu’a Tamkar Yiwa Kasa Ne – Inji Gwamna Masari


Shugabannin majalisun tarayyar Najeriya sun ziyarci Shugaba Buhari a London

Yayin da ‘yan Najeriya ke ta fadin albarkacinsu game da lafiyar shugaba Mohammadu Buhari, wanda yanzu haka ke London ana kulawa da lafiyarsa, gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yiwa shugaban addu’a.

Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa babu wani abu da zai sa su damu dangane da halin kiwon lafiyarsa, kasancewar likitoci sun ce yana bukatar hutu ne domin ya kara murmurewa bayan da suka gudanar da bincike akan rashin lafiyarsa.

A Najeriya dai shugabannin da malaman addinai sun yi ta kira ga ‘yan kasar da su rika yiwa shugaban addu’ar samun koshin lafiya da kuma komawa gida lafiya. Wanda hakan yasa shugaba Buhari aikewa da sako na musamman don nuna godiya da irin addu’o’in da yake samu.

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya umarci sarkin Katsina da sarkin Daura kan cewa ayi addu’a ta musamman shugaban Najeriya. A cewar gwamnan yiwa shugabanni addu’a abu ne da ya zama wajibi kuma sunna ce.

Domin karin bayani sauraron cikakkiyar hira da gwamna Alhaji Aminu Bello Masari da wakilin Muryar Amurka Zaharaddeen Sani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG