Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Dubban Mutane Zasu Fito Duba Akwatin Gawar Floyd


Masu zanga-zangar rike da Hoton fuskar George Floyd.

Masu makoki sun shirya haduwa a yau Litinin a birnin Houston na Amurka domin duban akwatin gawar Geroge Floyd bakar fatar Amurkan da ya mutu a hannun ‘yan sanda, lamarin da ya sabonta zanga zangar kin jinin cin zarafin ‘yan sanda a biranen Amurka da ma wasu wurare a fadin duniya.

A gobe Talata ne ake sa ran za a gudanar da jana’iza da binne Floyd.

Wani hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, yace dan takarar Democrat yana shirin zuwa Houston domin haduwa da iyalan Floyd ya kuma bada sakon bidiyo a wurin jana’iza.

A yanzu dai an janye sojoji a wasu jihohi da dama a kasar da aka gudanar da zanga-zanga bayan da aka yi ta samun arangama tsakanin masu zanga zangar da jami’an tsaro.

Dan majalisar dattawa a jami’iyar Trump ta Republican, Mitt Romney, ya fito cikin masu zanga zangar a jiya Lahadi.

Wannan shi ne karon farko da aka tabbatar da dan majalisa na Republican ya shiga zanga zanga da aka fara makwanni biyu da suka shige.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG