Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana sa ran mahaukaciyar guguwar teku ta Maria zata ratsa a Martinique da kuma Dominica


Mahaukaciyar guguwar teku
Mahaukaciyar guguwar teku

Ana sa ran mahaukaciyar guguwar teku da aka lakawa suna Maria zata ratsa a Martinique da kuma Dominica a daren yau Litini yayin da ruwan sama ke wucewa zuwa wasu yankuna da guguwar Irma tayi barna.

Cibiyar nazarin guguwa ta kasa a Amurka tace guguwar Maria tana da iska mai karfi dake juyawar kilomita 150 cikin awa guda, yayin da doshi Tsibiran Leeward, amma masu nazari suna sa ran zata kara karfi a yau Litinin.


Abin takaici itace guguwar zata shafi a tsibirai da dama inda Irma ta riga tayi barna, mako guda ko kuma kwanki goma da suka wuce, a cewar Dennis Feltgen na cibiyar nazarin guguwa ta kasa dake birnin Miami jihar Florida, yake fadawa Muryar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG