Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Samun Jan Kafa Wajen Komawar Yan Makaranta A Jihar Borno


Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 9 ga Satumba 2014.

A makon jiya ne dai gwamnatin jihar Borno ta bada sanarwar sake bude makarantun kwana na fadin jihar baki daya, wadanda aka rufe tun shekaru biyun da suka gabata sai dai yanzu haka ana samun jan kafa wajen komar dalibai musamman ma wadanda aka canzawa garuruwa zuwa garin Maiduguri.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya ziyarci makarantar Government College dake cikin garin Maiduguri, daya daga cikin makarantun da aka kawo wasu makarantu guda Tara daga wasu kananan hukumomi daban daban da kuma akace zasu ci gaba da gudanar da karatunsu a cikin wannan makaranta, sai dai daliban da suka sami dawowa a yanzu haka don ci gaba da karatun nasu kalilan ne.

Haruna ya zanta da wasu daga cikin shugabannin makarantu Shida cikin Tara da aka tura zuwa Government College dake garin Maiduguri, wanda kuma suka shaida masa irin kalubalen da suke fuskanta da kuma fatan da suke fatan da suke da shi na ci gaba da koyar da daliban nasu.

Suma wasu daga cikin daliban da Haruna ya zanta da su sunyiwa Allah godiya da rayuwar da suka sami kansu ciki, kasancewar suna da gurin kwana da abinci kuma karatu na tafiya yadda ya kamata.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG