Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Samun Karuwar Adadin Masu Kamuwa da COVID-19 a Najeriya


Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavurus a Najeriya ya kai 550 ranar Talata 8 ga watan Disamba, adadin dai shi ne mafi yawa da aka samu tun daga watan Agustan da ya gabata.

Yanzu haka mutune 2,225 ne suka kamu da cutar ta COVID-19 a cikin kwanaki 6 da suka gabata, lamarin da ke nuni da cewa an samu karin ne bayan makonnin da aka samu raguwar adadin masu kamuwa da cutar.

Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya kai 70,195, yayin da mutane 1,182 suka mutu.

A wata hira da Muryar Amurka, jagoran kwamitin ko-ta-kwana a yaki da annobar coronavirus a Najeriya Dr. Sani Aliyu, ya yi bayani game da damuwar hukumar akan karin yaduwar cutar da ake samu, inda ya ce a yanzu ana samun fiye da mutun 300 da suke kamuwa da cutar a kowacce a rana, ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuka.

"Shi ya sa mu ke yawan yin kira ga al’ummar Najeriya da su ci gaba da kiyaye matakan kariyar da suka dace, domin mutane sun saki jiki kuma har yanzu cutar na ci gaba da bazuwa," a cewar Dr. Aliyu.

Saurari cikakkiyar hirar Halima AbdurRa'uf cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG