Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Samun Raguwar Tashe-Tashen Hankulla A Kasar Kongo


Wata tawagar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton cewa an samu raguwar tashe tashen hankulla a yankin Kasai da ke Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Kungiyar kwararrun sun ce mai yiwuwa samun sauyi a bangaren hukumomin kasar zai iya bude Kofar zaman lafiyar da sansantawa a yankin mai fama da rikici.

Tawagar ta mika rahoton a yau Laraba game da halin da ake ciki yanzu a Kasai ga hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban tawagar kwararrun, lauyan dan kasar Senegalese, Bacre Ndiaye, ya ce yankin Kasai ya ci gaba da fama rikici da tashin hankali da laifuffuka da suka shafi cin zarafin bil adama.

Amma, ya ce, sabbin hukumomin kasar ta Congo sun himmatu wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata laifuka, abin da ya ce zai taimaka wajen yaki da masu aikata laifukan da ba su dace ba.

Sannan ya ce dan zaman lafiyar da aka samu a ‘yan watannin nan a yankin na Kasai ba dorarre ba ne.

"Ya ce munga yadda aka samu rikice-rikice a watan Fabrairun shekarar 2019, tsakanin dakarun kasar da Kamu mayakan Kamuina Nsapu ‘yan yakin sunkuru." Wannan wata alama ce da ke nuna cewa zaman lafiya ya samu tangarda, ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki su yi abin da ya dace.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG