Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Fara Babban Taron Shugabannin Duniya Na MDD


Babban taron shugabannin duniya na MDD
Babban taron shugabannin duniya na MDD

Daga ranar Litinin shugabannin Duniya za su hadu ta yanar gizo a babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD), yayin da za su tattauna matakin kasa da kasa domin dakile yaduwar coronavirus.

Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da coronavirus sun wuce miliyan 30, yayin da wadanda cutar ta kashe ya kusa miliyan daya a fadin duniya, bisa kididdigar jami’ar John Hopkins.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce yaduwar cutar coronavirus a duniya ta haifar da rashin daidaito tare da barazana ga ci gaban da aka samu tsawon shekara da shekaru.

Akwai taruka da za a gudanar sama da 80 duk ta yanar gizo, da zasu tabo dukkan batutuwan COVID-19, ciki har da babban taron da za a gudanar ranar 30 ga watan Satumba. Wanda babban Sakataren MDD da shugaban hukumar Lafiya ta Duniya WHO zasu jagoranta, tare da Birtaniya da Afirka ta Kudu, haka kuma taron zai mayar da hankali ga neman hanyar da hada karfi domin yakar annobar.

MDD ta kasance akan gaba kan yunkurin rage dumamar duniya, kuma shugabannin MDD sun ce shirin kare muhalli bayan coronavirus zai zamanto abu mai wuya ga duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG