Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Coronavirus Ta Takaita Yawon Bude Ido


'Yan Najeriya Na Dawowa Gida
'Yan Najeriya Na Dawowa Gida

Wani sabon rahota da hukumar kula da yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya (UNWTO) ta fitar jiya Talata na nuni da cewa, annobar coronavirus ta haddasa raguwar tafiye-tafiye a fadin duniya a farkon watanni shida na wannan shekara.

Bisa lafazin hukumar UNWTO, samun raguwar tafiye-tafiye daga watan Janairu zuwa watan Yuni na wannan shekara ya haifar da asarar dala biliyan 460 na kudaden shiga da ake samu daga masu yawon bude ido.

Wannan asara da aka samu ta ninka sau biyar wadda aka samu a shekarar 2009 lokacin da aka yi fama da matsalar tattalin arziki a fadin duniya.

Hukumar ta MDD ta fadi a wata sanarwa cewa, ta yi kiyasin cewa za a dauki tsakanin shekaru biyu zuwa hudu kafin tafiye-tafiyen yawon bude ido ya dawo daidai dana shekarar 2019.

Turai itace nahiya ta biyu da cutar tafi abkawa, inda yawon bude ido ya yi kasa da kashi 66 cikin dari a tsakiyar shekarar 2020. Yankunan Amurka da Afrika, da Gabas ta Tsakiya sun fitar da adadin raguwar yawon bude ido masu kama da juna.

“Wannan adadin na nufin ba a taba ganin irin wannan faduwar da yawon bude ido ya yi ba, biyo bayan rufe iyakoki da kasashe suka yi a fadin duniya kana suka takaita zirga zirga sakamakon annobar,” inji hukumar yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya.

Duk bangarori da kananan yankuna na duniya sun fuskanci durkushewar yawon bude ido na kasa da kasa sama da kashi 50 cikin dari, lamarin da ya jefa miliyoyin ayyuka da kasuwancin cikin hadari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG