Wani kwamitin zabe a Ghana, ya ce na'urar zaben Biometric da aka samar tun shekaru tara da suka gabata ta tsufa, kuma ba ta yin aiki sosai, don haka lallai akwai bukatar a tanadi sabuwa. Sai dai kuma wannan bayanin ya sha bamban da korafin hadakar kungiyoyin jami'yyun siyasa dake adawa da buga sabuwar rajistar masu zabe.
Daraktan fasahar sadarwa na babbar jam'iyyar adawa ta NDC Kwame Grifit, ya ce ko da yake tun a shekarar 2011 aka samar da na'urar, kuma an ci moriyar ta sosai har yanzu ta na aiki.
Daraktan ya kuma ce yana da muhimmanci a yi la'akari da cewa sau 81 kawai aka yi amfani da na'urar, da kuma sauran wasu kayan aikin na kwamfuta, amma hakan ba ya nufin sun tsufa.
Da yake mayar da martani, Atik Muhammed mamban kwamitin zaben ya karyata ikirarin, ya na mai cewa na'urorin ba su tashi aiki ba.
Don haka, hukumar zabe mai zaman kanta ta ke ganin ya dace a buga sabuwar ragistar masu zabe da za a iya dogara a kanta.
A saboda haka kwamitin ke ganin matakin hukumar zaben ya yi daidai, kuma ya zo kan lokaci. Mr. Muhammed ya kuma karyata ikirarin cewa buga sabuwar rajista tamkar barnar kudi ne. Ya na mai goyon baya ga hukumar zaben, akan ta kammala buga rajistar zabe akan lokaci don zaben kasar na wannan shekarar.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Accra, a Ghana.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Gwamnatin Nijar Ta Mayar Da Martani Game Da Tarzomar Zabe
-
Fabrairu 25, 2021
An Kama Masu Zanga Zanga Sama Da 200 a Nijar
-
Fabrairu 25, 2021
Ghana Ta Sami Kason Farko Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 23, 2021
NIJAR: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
-
Fabrairu 23, 2021
Wai Ko Wa Ake Ganin Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A Nijar?
-
Fabrairu 22, 2021
Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar
Facebook Forum