Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Wasu Manyan Jami'an Kasar Nijer da Sayen Jarirai Daga Kasashen Waje


A jamahuriyar Nijer an fara tuhumar masu sayen jarirai daga kasashen waje su mayar na su

Jaridar L'Evenement ce ta bankado labarin da ya yanzu ya ja hankulan mahukuntan kasar Nijer

Tun a cikin watan janairun shekarar 2014 jaridar L'Evenement ta bankado wannan labari na cewa wasu manyan jami'an kasar Nijer na zuwa kasashen waje su na sayen jarirai su na mayar da su tamkar 'ya'yan da suka haifa. Babban darektan jaridar ta L'Evenement Moussa Aksar yayi karin bayani a tattaunawarsu da wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Ko da yake dai har yanzu a hukumance babu wata majiyar jami'an tsaro, ko ta kotu da ta fito ta bayyana adadin mutanen da abun da ya shafa, wasu rahotanni sun ce tuni dai jami'an tsaro suka fara kiran wadanda ake zargi da hannu a sayen jarirai daga kasashen waje.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda ake tuhumar sun hada da tsoffin shugabannin manyan ma'aikatun gwamnati, da tsoffin ministoci da ministoci masu ci, da ma wasu masu manyan mukamai a majalisar dokokin kasar ta Nijer.

Abdoulaye Mamane Amadou yayi tattaki zuwa ofishin 'yan sandan farin kaya domin samun wani karin haske amma hakar shi ba ta cimma ruwa ba, sai dai ya ganewa idanun shi wasu mutanen da 'yan sandan suka fara yiwa tambayoyi akan wannan al'amari na sayen jarirai a kasashen waje.

Su ma kungiyoyin kare hakkokin bil Adama sun yi tir da Allah waddai da wannan al'amari. Malam Nouhou Arzika shugaban daya daga cikin irin wadannan kungiyoyi ya ce idan aka ci gaba da sayen 'ya'yan jabu kasar Nijer za ta koma kasar jabu. Sannan ya ce lallai a hukunta masu hannu a cikin wannan abun kunya komi matsayin su. Ya ce a bugi gawa, don mai rai ya ji tsoro.
XS
SM
MD
LG