Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru 19 da Tsagaita Wuta da Azbinawan Nijar


Yau ake bukin cika shekaru goma sha tara da gwamnatin kasar Nijer da ‘yan tawayen Azbinawa dake fafutukar aware domin neman yancin cin gashin kan arewacin kasar.

'Yan awaren arewacin Nijer na korafin rashin cika masu alkawari da gwamnati kasar Nijer tayi dangane da rajejeniyar sulhu da aka shima yau shekaru goma sha tara kenan

Tun daga wannan lokaci Kawo yanzu hankali da saman lafiya ya tabbata a arewacin kasar mai kunshe da arziki ma’adanai na karkashin kasa.

Wanna rajejeniya ta kasace wata mattatakalan kawo karshen rigingimun da yayi sanadiyar rasa rayukan dunbin mutanen da basu san hawaba basu san saukaba.

Tsohon madugun ‘yan tawaye malam Risa Abbula, yace “rana irin ta yau kamata yayi a bata mahimanci gaske kasancewa rana ce na zaman lifiya."

Daga wancen lokaci dai kawo yanzu ‘yan tawayen su sha kokawa kan yanda ake yi kafar angulu da,bukatocin su tare da kuma kin cika alkawari da gwamnatocin suka sha daukar masu dangane da wanna rajejeniyar.

Malam Risa Abbula, ya kara da cewa har yanzu akwai daruruwan matasa wadanda ke arewacin kasar da basu da aikin yi wanda hakan na daya daga cikin abubuwa dake iya bayana tashin hankali a arewacin kasar.

Gwamnar, yankin Agadas Garba Macido yace ”neman kwanciyar hankali shi yasa shugaban kasar ya tura shi yankin na Agadas ya kuma kara da cewa walahi yanzu sai muce Alhamdulilahi."
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG