Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Dar-Dar a Wasu Kauyukan Jihar Adamawa


Rahotanni dai sun bayyana cewa yanzu haka al’ummomin kauyukan Wadukun da Kwoh zuwa bangaren Tigno dake karamar hukumar Lamurde, cikin jihar Adamawan na cikin zaman dar-dar lamarin da yasa wasu mazauna yankunan kauracewa gidajensu.

Wani dan asalin yankin da ya nemi na sakaya sunansa, ya ce yanzu haka wasu jami’ansu na cikin daji, yayin da wasu kuma ke bakin kogi don gudun abin da ka iya faruwa, sakamakon bayanan da suka samu na cewa za’a kawo musu hari.

Wannan dai na zuwa ne a kasa da makwanni biyu da harin da aka kai wasu kauyukan Numan dake makwabtaka da Lamurde, inda aka samu asarar rayuka baya ga gidajen da aka kona.

Kawo yanzu duk kokarin ji daga bakin shugaban karamar hukumar ta Lamurde Mr. Vratis S Nzanzo, abin ya ci tura.

To sai dai kuma ita ma rundunar yan sandan jihar Adamawa ta bakin kakakinta SP.Othman Abubakar, ta ce bata da cikakken bayani, to amma ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG