Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Wata 'yar Najeriya Da Kashe Ma'aikacin Shige Da Fice A Sudan


Wata Yarinya

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da sanawar cewa wata haifaffiya Najeriya 'yar asalin Kasar Sudan Inas Maikano Khalid ce ta kashe ma'aikacin shige da fice Habibu Almu a gidanshi dake Khartoum.

A cewar kafar yada labaran oaktvonline, mai magana da yawun ma'aikatar Dakta Tope Elias-Fatalie ne ya bada wannan sanarwar a jiya a garin Abuja, inda ya kara da cewa wacce ake zargin daliba ce a wata jami'a dake Khartoum kuma tana hannun jami'an tsaro ana gudanar da bincike.

Bayan kuma tsananin bincike wacce ake zargin ta amsa laifin ta inda aka gano cewa ta kashe shi ne ta hanyar daba masa wuka, daga bisani kuma tayi mishi sata ta gudu.

A halin yanzu dai ana shirye shiryen dauko gawar Habibu zuwa Najeriya domin a binne shi kamar yadda addinin sa ya umarta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG