Idan 'yan majalisar basu dauki matakan dawo da kudaden ba 'yan kungiyar na kiran hukumar EFCC ta binciki zargin ta kuma gurfanar da duk wadanda aka samu da laifi gaban kuliya.
Masu zaman dirshen din dai har ma barazana suka yi na daukan wasu matakai nan gaba da suka hada da hana 'yan majalisar shiga ko fita daga majalisar. Sun kuma ce su ba 'yan amshin shatan Abdulmummuni Jibrin ba ne.
Ibrahim Garba Wala na cikin masu zaman dirshen din kuma yayi bayani. Yace 'yan majalisar sun fada cewa su ne suke nada shugaban EFCC su ne kuma suke warware nadin saboda haka Wala yace ba zasu zubawa 'yan majalisar ido ba suna wawure dukiyar kasa.
Wai su kansu 'yan majalisar sun fada cewa alawus din da suke karba bai dace ba idan kuma an sani ana iya dauresu.Abun da su keyi cikin siri yanzu ya fito fili kuma 'yan Najeriya basu yadda ba. Sun ba 'yan majalisar mako biyu ko su mayar da kudin ko su kai kansu a yi masu hukumci.
Cikin masu dirshen din har da wani da ya fito daga Kiru a jihar Kano mazabar shi Abdulmummuni Jibrin. Yace bai yadda da irin alawus da ake ba 'yan majalisa ba alhali kuwa yara na can babu ilimi ga kuma yunwa tana damun mutane.
Amma na hannun daman kakakin majalisar Onarebul Abubakar yace masu zanga zangar na shiga sharo ne ba shanu. Yace hatta shi Jibrin din ba zai yi wani tasiri ba saboda ya hainci mutane ya kuma zalunci mutane. Wai tunda aka cireshi ya hau dokin zuciya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.