Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Jami'an Tsaro Da Bindige Wani Dalibin Sakandare A Birnin Yamai


Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Kungiyoyin dalibai a birnin na Yamai sun yi kira da a kauracewa ajujuwan karatu har sai an gudanar da kwakkwaran bincike.

A Jamhuriyar Nijar, ana zargin jami’an tsaro da halaka wani dalibi a birnin Yamai a lokacin da suka bude wuta akan motar daliban wata makarantar sakandare dake zagayen tallata wani bikin da suke shirin gudanarwa.

Wannan lamari da ya faru a ranar Talata ya sa kungiyar dalibai kiran magoya bayanta su kauracewa azuzuwan karatu daga ranar Talata sai yadda hali ya yi.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai
Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Mummunan al’amarin ya faru ne gab da makarantar sakandaren CEG Bagdad da aka fi sani da CES France Amitie Niger dake unguwar Recasement lokacin da wata mota kirar marsandi dauke da daliban makarantar sakandaren le Niger De Demain suke zagayen manna hotunan wani bikin da suke shirin gudanarwa a cewar Maiga Mounkaila na kungiyar daliban makarantun sakadaren ta Yamai.

Ya ce lokacin da ya isa wurin ya tarad da mota tana hayaki kamar wacce ta kone sakamakon harbin bindiga, yaran dake cikinta su biyar samari biyu da budurwa daya, a baya mutun guda da dreba suna gaba kawai sai yaji suna kururuwa suna cewa yaro ya mutu. Daya tambaye su me ya faru sai suka ce wuta aka bude masu.

Dangin wannan yaro mai sunan Nouridine dake ajin karshen makarantar share fagen shiga jami’a ta CSP NDD sun garzaya wurin da abin ya faru cikin yanayin bacin rai.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai
Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Lokaci kadan bayan faruwar wannan al’amari ‘yan sanda sun dauki gawarsa zuwa asibiti inda aka bayyana cewa za a gudanar da bincike a likitance domin gano ainihin masabbabin mutuwar Yaroslavl yayinda motar dake dauka da su ke nuna alamun harbin harsasai a kalla uku.

Hakan ya sa kungiyoyin dalibai kiran taron gaugawa wanda daga karshe suka umurci magoya bayansu su kauracewa ajin karatu har sai gaskiya ta bayyana.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai
Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Ya ce ba zasu yarda ba, ya kamata a yi shara’a , ba zasu zuba ido suna kallon irin wannan mummunan abubuwa suna wakana a kasa ba. Abin bakin ciki ne su je mana su fatataki mayakan jihadi da ‘yan boko haram amma su fararen hula azo ana kashe su. Gaskiya ya kamata a fiddo masu hakkinsu.

Wannan na faruwa ne mako guda bayan da daliban Nijer suka yi taron tunawa da wasu dalibai uku na jami’ar Yamai wadanda jami’an tsaro suka bindige a yayin wata zanga zangar 1990 inda shekarun 32 bayan wannan kisa har yanzu an kasa hukunta masu hannu a wannan danyen aiki.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Jami'an Tsaro Sun Bindige Wani Dalibin Sakandare A Birnin Yamai
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG