Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Aka Ceto Daga Hannun Masu Safarar Mutane Zuwa Kasashen Ketare Sun Yi Nadama


Safarar Mutane
Safarar Mutane

Matasan da hukumar yaki da safara da fataucin bil’adama ta Najeriya NAPTIP ta ceto daga hannun masu safarar mutane yayin kokarin tsallakawa da su kasar Libya, sun bayyana nadama tare da yin gargadi ga ‘yan uwansu matasa.

Masu safarar mutane sun yi gargadi wa ‘yan uwansu matasa ne game da hadarin dake cikin tafiyar.

Tun da daga farko hukumomin tsaro na Jamhuriyar Nijar ne sukayi nasarar ceto matasan su 61 a yankin Mai’adua na kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar ta Nijar, yayin da masu kitsa fataucin matasan ke kokarin tsallakawa da su akan hanyar su ta zuwa Libya.

Matasan waanda suka hada maza da mata, yanzu haka sun yi nadama game da halin da suka tsinci kansu.

Dawo da matasan na daga cikin sakamako mai alfanu daga aiki tsakanin hukumar NAPTIP mai yaki da fataucin bil’adama ta Najeriya da hukumomin tsaro na ketare musamman kasashe da ake makwabtaka da du irin su Nijar, inji Mr Yohana Haruna Jagoran jami’an NAPTIP dake sintiri na musamman a shiyyar Kano.

Yanzu haka dai wadannan matasa sunyi janhankali ga ‘yan uwan su masu kwadayin zuwa kasashen wajen domin neman kudi.

Masu Safara Da Mutane Sunyi Gargadi Wa Matasa Game Da Hadarin Tsallake Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG