Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Shugaban Kungiyar Agaji Na Amnesty International Da Ta'addanci


Amnesty International
Amnesty International

Hukumomin kasar Turkiyya sun kame shugaban kungiyar bada agaji ta Amnesty International, wanda suka ce yana jiran a soma shari’ar zargin da ake mishi na zama dan wata kungiyar ta’addanaci, a cewar kampanin dillacin labaran A-P wacce ita kuma ta sami labarin daga kampanin dillacin labaran Anadolu na gwamnatin Turkiyyar.

Sai dai har yanzu shi kampanin gwamnatin bai maido amsa ba ga gayayattar da tashar rediyon VOA tayi mishi na ya tabattarda kamun da akace anyi wa shi Taner Kilic, wanda kuma wanda tun ran Talata yake tsare.

Kungiyar Amnesty dai ta ce kama ma’aikacin nata kamar wani mataki ne na “rena shari’a” ne.

An dai kama Kilic tareda wasu lauyoyi ne a yamamcin kasar bayanda aka zarge su da laifin anfani da wata fasaha da ake kira “ByLock,” wata fasahar juye ma’anar kalimomi da sakkonin da ake aikawa ta hanyar gizo, wanda kuma ake zargin shine magoya bayan shehin malamin nan Baturkiye dake zaune a nan Amurka, Fethullah Gulen suka yi anfani da shi.

Shi Gulen dai shine hukumomin Turkiyyar ke zargida jagorancin yunkurin juyin mulkin da baici nasara ban a bara, abinda Gulen din ya sha musantawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG