Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Masu Ra'ayin Mazan Jiya Na Fuskantar Koma Baya a Zaben Birtaniya


Masu kada kuri’a a Birtaniya sun kawowa jam’iyyar masu ra’ayin yan mazan jiya mai mulki ta Firai Minista Theresa May koma baya, a zaben da ta nema a gudanar da nufin neman goyon bayan tattaunawar da za a yi dangane da ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Sakamakon farko na zaben na nuni da cewa, kasadar da May tayi na kira a gudanar da zaben da wuri ya gamu da matukar cikas, inda jam’iyarta ke fuskantar barazanar rasa rinjaye a majalisa. Wata kungiyar kafofin watsa labarai ne ta gudanar da binciken, bisa ga tambayoyin da suka yiwa wadanda suka kada kuri’a yayinda suke barin mazabu a duk fadin kasar.

Idan haka ta babbata, sakamakon zaben zai zama abin kunya ga May, wadda ta sa a gudanar da zaben shekaru uku kafin cikar wa’adi, da begen samun Karin kujeru da rinjayen da take dashi, da kuma kara samu karfin guiwa a tattaunawar Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai. Idan hakarta bata cimma ruwa ba, mai yiwuwa a matsa mata lamba tayi murabus.

Ana harsashen cewa, jam’iyar masu ra’ayin rikau zata sami kujeru dari uku da goma sha hudu, yayinda jam’iyar hamayya ta Labor zata sami kujeru dari biyu da sittin da shida. An yi kiyasin cewa, jam’iyar Scottish national zata sami kujeru talatin da hudu, yayinda jam’iyar masu sassauci ra’ayi kuma zasu tashida kujeru goma sha hudu.

Idan aka tilastawa May tayi murabus bayan watanni goma sha daya da hawanta karagar mulki, wa’adin mulkinta zai kasance mafi gajarta a tarihin kasar tun daga shekara ta dubu da dari tara da ishirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG