Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anambra: Dan Takarar Gwamna Ya Ki Ya Zabi Kansa, Ya Jefawa Soludo Kuri'a


Akachukwu Nwankpo, dan takarar jam'iyyar ADC (Facebook/ Akachukwu Nwankpo fans club)
Akachukwu Nwankpo, dan takarar jam'iyyar ADC (Facebook/ Akachukwu Nwankpo fans club)

A cewar Nwankpo, bisa zabin kansa ne ya yanke shawarar jefa kuri’arsa ga Soludo saboda ya san jam’iyyarsa ba za ta kai labari ba.

Mista Akachukwu Nwankpo da ke takarar kujerar gwamna a jihar Anambra karkashin jam’iyyar ADC, ya jefawa abokin hamayyarsa na jam’iyyar APGA Farfesa Charles Soludo kuri’a.

Hakan na nufin ba zabi kansa ba kenan a karashen zaben da aka yi a ranar Talata a karamar hukumar Ihiala da ba a yi zabe ba.

A cewar Nwankpo, bisa zabin kansa ne ya yanke shawarar jefa kuri’arsa ga Soludo saboda ya san jam’iyyarsa ba za ta kai labari ba.

A ranar Lahadi, hukumar zabe ta INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben da aka yi a ranar Asabar inda ta ce sai an yi zabe a Ihiala kafin ta ayyana wanda ya lashe zaben.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Nwankpo ya kada kuri’arsa a mazaba ta 004 da ke Umuapani Ward, amma ya tuntubi matasa kafin daukan wannan mataki.

Amma ya kara da cewa bai tuntubi jam’iyyarsa ba kafin daukan wannan matsaya.

Farfesa Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe kananan hukumomi 18 cikin 21 da jihar ta Anambra ke da su.

Hakan ya sa tuni masu hasashe suka hango masa nasara a wannan zabe da jam’iyyu 18 suka tsayar da ‘yan takara ciki har da Nwankpo da ya zabi Soludo.

XS
SM
MD
LG