Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamna A Anambra


Zauren tattara sakamakon zabe a jihar Anambra (Channels TV - Video snapshot)
Zauren tattara sakamakon zabe a jihar Anambra (Channels TV - Video snapshot)

Izuwa lokacin hada wannan rahoto, an kidaya kananan hukumomi tara. cikin 21 da jihar ta Anambra ke da su.

Rahotanni daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa Malaman zabe na ci gaba da hada kan kuri'un da aka kada a zaben gwamnan da aka yi a jihar.

‘Yan takara 18 ne suke kokarin maye gurbin gwamna Willie Obiano wanda ya kammala wa’adinsa na biyu.

Zaben na Anambra ya gudana cikin lumana duk da cewa an dan samu ‘yar hatsaniya nan da can baya ga matsalar tangardar na’ura tantance masu kada kuri’a da aka fuskanta.

Dan takarar jam’iyyar APGA Farfesa Charles Soludo ya kwashe sa’o’i da dama kafin ya kada kuri’ar kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kazalika, ministan kwadago Chris Ngige ma ya fuskanci matsalar ta na'ura a lokacin da ya je kada kuri'arsa.

Matsalar na’urar ta sa hukumar zabe ta INEC ta fitar da sanarwar tsawaita lokacin rufe rumfunan zabe.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto, an kidaya kananan hukumomi bakwai.

Jihar Anambra na da kananan hukumomi 21.

Rahotanni sun ce yayin da ake hada hancin sakamakon ana karasa kada kuri’a a wasu yankuna da aka samu matsalolin da suka shafi na na’ura da zuwan kayan zabe a makare.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG