Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Annobar COVID-19 Na Kara Tsananta A Wasu Kasashen Duniya


Da alamar dai hauhawar annobar COVID-19 da aka yi hasashen zai fara yayin da yanayin sanyi ke karatowa a bangaren duniya da ke arewa da kuryar equator, yana kan faruwa.

Yanzu a kowacce rana ana samun wadanda da suka kamu da cutar 330,000 a duniya, yayin da yankunan Turai da Amurka suke fuskantar hauhawa mai ta da hankali.

A Amurka, babban masanin cututtuka masu yaduwa a kasar ya shaida wa wa Amurkawa cewa, su sake tunani game da shirye-shiryensu na bikin cika ciki da ake kira Thanksgiving a karshen watan Nuwamba, lokacin da mutane da yawa, bisa al'ada, suke tafiye-tafiye ta cibiyoyin jigila, kamar tashoshin bas, tashar jirgin kasa, da filayen jiragen sama don kasancewa tare da danginsu.

"Idan kuna da ‘yan uwa masu rauni, tsofaffi ko mutanen da ke cikin mawuyacin hali, ya kamata ku yi la'akkari da ko ya kamata ku yi hakan a yanzu," abin da Fauci ya fada wa tashar talabijin ta ABC News kenan.

Ya kuma bai wa al’umma shawarar da ya kamata watakila su jinkirta shirye-shirye kuma "su jira" har sai an shawo kan annobar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG