Accessibility links

Anya Kuwa Zaben Kananan Hukumomi Zai Yiwu a Borno Tsakanin Watan Afrilu da Yuli?


Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima.

Ra'ayoyin manyan shugbannin siyasar jahar Borno sun bambanta game da yin zaben kananan hukumomi

Gwamnan jahar Borno Kashim Shettima ya bayyana aniyar gudanar da zabe a kananan hukumomin jahar ishirin da bakwai tsakanin watan afrilu da yuli mai zuwa.


An dade ba a yi zaben kananan hukumomi a jahar ta Borno ba saboda rigingimu da tashe-tashen hankulan da su ka sa shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a jahar ta Borno da makwaftan ta biyu wato Adamawa da Yobe.

Wakilin Sashen Hausa a jahar Borno Haruna Dauda Biu ne ya aiko da wannan rahoto.
XS
SM
MD
LG