Accessibility links

Ranar Litinin Za'a Nada Sabon Shugaban Jam'iyar PDP

  • Halima Djimrao

hoton helkwatar jam'iyar PDP

Mataimakin shugaban jam'iyar ta PDP Uche Secondus zai yi rikon kwarya har zuwa ranar litinin

Ta dai tabbata gaskiya cewa Bamanga Tukur yayi murabus daga mukamin shugaban jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya kamar yadda sakatatren yada labaran jam'iyar Olisa Metuh ya ke kara jaddadawa bayan wani taron shugbannin jam'iyar:


'Yan jam'iyar ta PDP sun yi godiya ga Bamanga Tukur saboda matakin da ya dauka na yin murabus domin raya jam'iyar.

Tuni dai har an fara rade-radin cewa ana sa ran nada Bamanga Tukur sabon jakadan Najeriya a Kasar Sin wato China.

Wakilin sashen Hausa a Abuja Nasiru Adamu el-Hikaya ne ya aiko rahoton.
XS
SM
MD
LG