Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ba Za Ta Iya Gudanar Da Babban Taro Ba Tare Da Rudani Ba – Sule Lamido


Babban taron PDP ya caza manyan ‘yan jam’iyyar da nuna babu barin baya da ‘kura da zai shafi tasirin jam’iyyar a zaben shekarar 2019.

Jigon jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya ce jam’iyyar APC ba zata iya gudanar da babban taro ba tare da rudani ba.

Wannan furuci dai ya biyo bayan kushe taron da kakakin APC, Bolaji Abdullahi yayi da kuma nuna cewa PDP bata koyi darasi ba kan ‘dabi’arta ta ‘dauki ‘dora. Lamido ya ce APC da taimakon PDP ta lashe zaben shekarar 2015.

Shima tsohon sakataren ANPP da tuni ya koma jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar Kumo Garkuwan Gombe, yace yana yiwa shugaba Buhari fatan Alheri, amma ya na ganin har yanzu ra’ayin Buharin bai fita daga ‘dabi’un sojoji ba.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG