Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Zabi Kashim Shettima Don Zama Mataimaki Na A Takarar Shugabancin Najeriya Don Ya Cancanta-Bola Tinubu


Buhari, (hagu) Tinubu, (tsakiya) da gwamna Masari a dama.
Buhari, (hagu) Tinubu, (tsakiya) da gwamna Masari a dama.

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Najeriya mai zuwa na 2023 Bola Ahmed Tinubu ya ce ya zabi tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima ya zama mataimakin sa a takarar don ya cancanta ne.

Tinubu ya bayyana haka ne bayan ganawar sirri da shugaba Buhari a Daura kan zabar wanda zai zama mataimakin da a ke ta muhawara da tunanin daya daga gwamnonin da ke gado ne zai samu.

Tinubu ya ce bai tuntubi Kashim ba gabanin ayyana shi a matsayin mataimakin takarar, amma ya shaidawa shugaba Buhari.

Don na ga ya cancanta ne, zai iya kuma za a iya amincewa da shi” Inji Tinubu a takaitacciyar zanatawa da manema labaru.

Buhari, Tinubu da Shettima
Buhari, Tinubu da Shettima

Matakin ya tabbatar da bayanan tsohon dan takarar mai rikwan kujera wato Ibrahim Kabri Masari da ke nuna sai bayan sallah za a yi hakan da shawarar shugaba Buhari.

Yanzu dai ta tabbata kenan za a yi takarar ta musulmi da musulmi a inuwar APC a kasar da addini kan taka rawa wajen lamuran yau da kullum.

Masari ya ce son samu ‘yan Najeriya su rika bin wanda zai yi adalci ba duba addini ko kabila ba.

Shettima wanda tsohon gwamnan Borno ne, shi ya tsayar da gwamna Zulum mai ci a 2019 inda wasu ke cewa yaro ya fi maigida farin jini, amma wasu na duba gogewar Shettima a lamuran kasa waje da batun tsaro na jihar Borno.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

XS
SM
MD
LG