Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Da PDP Sun Kasa Tsaida 'Yan Takarar Mataimakan Gwamna A Zaben Anambra - Obiano


Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA.
Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA.

Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya kalubalanci jam’iyyun APC da PDP da cewa har yanzu ba su shirya shiga takarar da ka iya ba su nasara a zaben gwamnan jihar da za'a gudanar ba.

Gwamnan ya yi wannan kalami na sa ne biyo bayan kwashe makwanni biyu da gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun biyu, amma har yanzu ba su sanar da mataimakan 'yan takarar nasu ba, yana mai cewa hakan na nufin cewa ba su shiryawa yin takarar ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yadda labarai da wayar da kan al’umman jihar Anambra, Mr. C. Don Adinuba, ya rattabawa hannun inda ya ruwaito gwamna Willie Obiano na cewa, irin wannan matsayin na rashin shiryawa shiga takara gadan-gadan zai ba jam’iyyarsa, ta APGA nasara a zaben jihar mai zuwa.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, zaben fitaccen masanin tattalin arziki kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Chukwuma Charles Soludo, da jam’iyyar APGA ta yi a matsayin dan takarar gwamna, ya rudar da sauran jam’iyyun inda suka kasa fidda abokan takarar su.

Karin bayani akan: APGA, INEC, Willie Obiano, APC, PDP,jihar Anambra, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA
Charles Soludo ya lashe zaben fidda gwani na APGA

Dan takarar gwamnan jam’iyyar APGA, Farfesa Soludo, ya ayyana abokin takarar sa mai suna Dakta Onyeka Ibezim, kwararren likita kuma kwararre a fannin kera-kere.

A ranar 6 ga watan Nuwambar shekarar 2021 ne hukumar zaben Najeriya wato INEC ta tsaida na gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra din.

XS
SM
MD
LG