Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC: Hukumar Zaben Najeriya Ta Ki Karbar Sunayen ‘Yan Takarar Zamfara


Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

Daidai lokacin da a ke muhawara kan karbar sunayen ‘yan takarar zaben 2019 na APC daga jihar Zamfara, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya ce hukumar ba za ta ce komai ba tun da wadanda lamarin ya shafa sun kai kara kotu, amma sam hukumar ba ta karbi sunayen ba.

Farfesa Yakubu na magana ne kan rade-radin cewa jam’iyyar APC ta mika sunayen ‘yan takarar ta daga kan na gwamna zuwa ‘yan majalisar Dattawa da Wakilai, da tun farko hukumar ta ce ba za ta amshi sunayen don saba ka’idar lokacin gudanar da zaben.

Jigo a siyasar APC ta Zamfara Ikra Aliyu Bilbis, ya ce sun kalubalanci matsayin hukumar zaben a kotu don su na da yakinin an gudanar da zaben, da sa ran samun hukunci a ranar Talatar nan.

A tarihi idan hukumar zabe ta dauki mataki kan lamari irin wannan, kotu ce kan zama raba gardama kuma ko ma ta yaya shari’ar ta kaya, ba mamaki wanda bai gamsu ba ya tafi kotun daukaka kara.

Domin Karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG