Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Na Barazanar Kai Shugabannin 'Yan Awarenta Kotu


Kimanin makon guda da kaddamar da bangare a Jam'iyyar APC, wato R-APC, jam'iyyar ta ce za ta daukin matakin gurfanar da Buba Galadima da ke jagoranta bangaren a gaban kotu.

Tun farko Shugaban APC, Adams Oshiomole ya so shashantar da batun na sabuwar APC, dama Buba Galadima ya yi tsinkayin hakan ka iya faruwa.

"Mu ne halattatun shugabannin APC ba su ba don su ba zabesu bisa halarci ba - 'Yan Agola ne su. Idan suna da wata magana da ba su yarda da mu ba, su tafi kotu za mu samesu a can, mu tabbatar musu cewa mu ne 'ya'yan halal," inji Galadima

Mataimakin shugaban APC na Arewa, Lawali Shu'aibu ya ce duk barazana ba zata shafi nasarar Shugaba Buhari ba.

"Wallahi bamu da wata fargaba game da 2019. Ina tabbatar maka in har Buhari ne dan takararmu na shugaban kasa, zamu je mu kwanta mu ta bacci," inji shi

A cewarsa, za su yi haka saboda suna da kwarin gwiwa akan Buhari idan aka yi la'akkari da halin da kasar ke ciki.

"In ba shi ba, ba wanda zai iya rike kasarnan akalla dai daga yanzu zuwa shekaru hudu da ke gabanmu, " inji Lawali Shu'aibu.

Dattijo a APC Sanusi Baban Takko, ya shawarci APC da Shugaba Buhari da su rika la'akkari da lamuran siyasa.

"Ba wai mu na son Buhari ya fadi ba ne. Ai da bamu sonshi da ba mu shiga APC ba. Amma muna tsoron kada wani wanda ba mu tsammani ya zo ya kada Buharin. Don yana iya faduwa. Matsayi na Allah ne, mai ba wanda ya ga dama," inji Sanusi Baban Takko.

Masana harkokin siyasa sun yi hasashen wannan wata hanya ce da 'yan jam'iyyar APC za su samu damar ficewa zuwa jam'iyyar PDP ko wasu jam'iyyun adawa musamman wadanda ke fargaban ba za su samu tikiti daga jihohinsu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG