Accessibility links

APC Ta Ce Lallai A Soke Zaben Gwamnan Jahar Anambra


Tambarin jam'iyar APC ta hamayya a Najeriya

Babbar jam'iyar APC mai hamayya a Najeriya ta yiwa hukumar zaben kasar zanga-zanga a kan zaben gwamnan jahar Anambra

'Yan jam'iyar hamayyar APC sun yi jerin gwano zuwa ofishin hukumar zaben Najeriya mai zaman kan ta, INEC, a takaice domin su mika ma ta bukatar su ta neman lallai ta soke zaben gwamnan jahar Anambra wanda dan takarar jam'iyar ta APC Chris Ngige ya zo na uku. Shugabannin jam'iyar sun yi kokarin shiga harabar hukumar zaben amma hakar su ba ta cimma ruwa ba saboda jami'an tsaro masu ban tsoro sun tare hanyar shiga. Wakilin Sashen Hausa a Abuja Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko da cikakken rahoton da za ku ji kamar haka:


Babu wani jami'in hukumar zaben da ya fito ya karbi shugabannin jam'iyar APC, ya ji bukatun su da koken su, ballantana kuma har manema labarai su samu tattaunawa da su.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kan ta, INEC, ta tsayar da cewa asabar din nan mai zuwa za a yi zaben cikace wanda aka yi a ranar goma sha shida ga watan Nuwamba.
XS
SM
MD
LG