Accessibility links

Murtala Nyako Yace Sun Yada Kwallon Mangwaro Ne Don Su Huta da Kuda


Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja

Gwamnan na Jihar Adamawa yace gwamna Sule Lamido na Jigawa da Babangida Aliyu na Jihar Neja sun ce a yanzu ba su shirya ba ne kawai...

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, ya bayyana cewar canja shekar da suka yi daga jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya zuwa babbar jam'iyyar hamayya ta APC, tamkar yasar da kwallon mangwaro ne domin hutawa da kuda.

Gwamna Nyako, yace su gwamnoni 5 na PDP-Sabuwa da suka yanke shawarar komawa cikin jam'iyyar APC sun gamsu da tattaunawar da suka yi da shugvabannin APC.

Da yake magana a kan sauran gwamnoni biyu na PDP-Sabuwa da ba su bayyana komawa cikin jam'iyyar APC a yanzu ba, watau gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa da Babangida Aliyu na Jihar Neja, gwamnan na Adamawa yace takwarorin nasu sun bayyana cewa ba su shirya komawa hamayya ce a wannan lokacin ba, kuma daya daga cikinsu ma ya bayyana cewa watakila zai biyo sawunsu ya koma APC a cikin watan Janairu.

Ga rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Yola...

XS
SM
MD
LG