Accessibility links

Ana iya cewa jam'iyyar APC ta kama hanyar jam'iyyar PDP domin ta dare gida biyu a Jihar Neja kafin ma tafiya ta yi nisa.

Sabuwar jam'iyyar adawa a Najeriya APC ta dare gida biyu a jihar Neja dake arewacin kasar.

Makon jiya ne wasu 'ya'yan jam'iyyar ta APC suka yi wani taro inda suka zabi Alhaji Ibrahim Bako Shettima a matsayain shugaban jam'iyyar a jihar Neja na riko tare da wasu mukarrabansa guda hudu.To sai dai ranar Litinin din nan wasu 'ya'yan jam'iyyar su ma suka yi taro inda suka zabi Alhaji Baba Aminu a matsayin shugaban jam'iyyar tare da mukarrabansa guda hudu.

Alhaji Umar Sha'aibu tsohon shugaban rusarshiyar jam'iyyar APC wanda yake bangaren Alhaji Ibrahim Bako Shettima ya ce zaben da suka yi halartacce ne. Ya ce shugabannin APC na kasa sun san wanene sahihin shugaban jam'iyyar a jihar Neja. Ya ce su ne kuma zasu fadi wanda suka yadda da shi. Tabbas sun yi zabe kuma kawo yanzu babu wanda ya ce zaben haramtacce ne. Dangane da wasika da aka ce uwar jam'iyyar ta aiko sai Alhaji Sha'aibu ya ce ta bogi ce.

A wata sabuwa kuma Alhaji Ibrahim Musa dan majalisar dattawan Najeriya ya halarci taron ranar Litinin inda aka zabi Alhaji Baba Aminu. Ya ce wannan taron da shi ya kasance a wurin shi ne ingantace kuma halal. Shi ne kuma sahihi saboda hedkwatar jam'iyyar ta APC ta aiko masu sa ido. Haka ma INEC ta sa ido a taron zaben. Bugu da kari a cikin mutane talatin da daya guda ashirin da daya sun kasance a taronsu na ranar Litinin din nan. Tambayarsa ita ce mutane goma ne zasu fi ashirin da daya?

Alhaji Abubakar Lado shi ne shugaban matasan jam'iyyar a Najeriya da ya wakilci uwar jam'iyyar daga Abuja. Ya ce uwar jam'iyya ta rubuta wasika kuma ta bashi ya gayawa bangaren Shettima cewa jam'iyyar bata san da taronsu ba bata kuma amince da su ba. Ya ce haraka ce ta jam'iyya don haka sanadiyar zaben da ya tsayar da Baba Aminu za'a kafa kwamitin dattawa ya kawo sulhu. Ya ce zasu sa a kirasu a ji menen hanzarinsu na yin zabe makon da ya wuce ba tare da sanin hedkwatar din jam'iyyar ba.

Masana harkokin siyasa sun ce wannan lamarin babban kalubale ne jam'iyyar ta fara cin karo da shi a jihar Neja musamman ganin yadda manyan 'yan siyasa na bangaren Shettima suka ja daga suka nace kan wanda suka zaba.

Mustapha Nasiru Batsari nada rahoto.

XS
SM
MD
LG