Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Nemi Gafara


Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa
Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa

A kokarinsu na jawo 'yan tawayen gwamnonin PDP jam'iyyar APC ta saba ma wasu 'ya'yanta a Sokoto da Kano

Jam'iyyar APC ta kafa wani kwamiti karkashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Edo John Oyegun ya nemi gafara wurin tsoffin gwamnonin Sokoto da Kano.

Kwamitin da ya kunshi gwamnan Zamfara Yari da tsohon kakakin majalisar walikan Najeriya Alhaji Aminu Masari ya ziyarci Sokoto inda ya gana da 'yan jam'iyyar. Gwamnan Zamfara Alhaji Yari ya ce yayin da shugabannin jam'iyyarsu ta kasa suka ziyarci Sokoto a kokarinsu na san jawo gwamnonin PDP bakwai da suka buturewa jam'iyyarsu ta PDP zuwa tasu, 'yan jam'iyyar sun yi korafin ba'a bi ta kansu ba.

Gwamna Yari ya ce idan akwai wadanda ransu ya baci sabili da abun da ya faru uwar jam'iyya tana neman gafara. Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce idan an yiwa mutum laifi aka dawo neman gafara to sun yafe. Ya ce duk wani dan siyasa a Sokoto shi ya taba zama ubangidansa. Don haka idan yaron gida ya ce yana son ya dawo kuma ba tilasta masa aka yi ba, idan ya zo za'a duba a ga ko ya cancanta.

'Yan jam'iyyar sun ce bayan jam'iyyarsu ta kafu basa bukatan wasu bata gari da suka kira agwagi masu bata ruwqa.

Umar Faruk Sanyinna nada rahoto.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG