Accessibility links

Yawan canza sheka da 'yan siyasan Najeriya ke yi suna musayan gurabensu ya sa wasu sun soma shakkar ko suna da akida kuwa

A 'yan kwanakin nan 'yan Najeriya sun ga yadda 'yan siyasa ke fita daga jam'iyyarsu zuwa wata jam'iyyar wadda a da can sun yi kyamarta. To ko menene dalilin hakan?

Yayin da zaben shekarar 2015 ke kara karatowa 'yan siyasa kuwa sai kara jan daga suke yi musamman tsakanin jam'iyyun PDP da APC. Kowace jam'iyya ji take ita ce zata lashe zabe mai zuwa. Kowace jam'iyya nada madogararta. PDP na jin ita ce ke rike da madafin iko a yanzu domin haka zata ci zabe. Ita kuma APC tana ganin tun da ta cafke jihohin kudu maso yamma banda jihar Ondo kuma wasu gwamnonin PDP biyar sun koma jam'iyyar to babu shakka zata ci zabe.

Sai dai 'yan Najeriya sun damu da yadda akidar siyasa ke neman bacewa a Najeriya domin yawan canjin shekar da ake gani yana faruwa a kasar. Lamarin ya zame kamar wasan kwaikwayo. Kafin guguwar canza sheka ta taso idan an saurari wasu 'yan siyasa sai a yi tsammanin babu abunda zai rabasu da jam'iyyarsu. To sai dai lamarin ya canza yanzu domin kwaram ga shi suna canza kalamai kamar ba su ba ne.

Siyasar Najeriya ta zama abun kallo domin bayan gwamnonin PDP biyar da suka koma APC wasu 'yan majalisar wakilai sun bi sawunsu kana wasu tsofofin gwamnoni suka fice daga APC zuwa PDP. Daya daga cikin tsofofin gwamnonin Alhaji Attahiru Bafarawa a jawabin da ya yi bayan an karbeshi zuwa PDP ya ce ya gayawa shugaban kasa idan yana da shakka a jiharsa ta Bayelsa to yana da shakka a jihar Sokoto.

A jihar Adamawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ya taba ficewa daga PDP ya kuma koma sai gashi ya sake ficewa zuwa APC. Shi ma ya ce wai PDP ta daina sauraran jama'a, ta yi nisa bata jin kira shi ya sa ya bar jam'iyyar.

'Yan Najeriya sun soma tambaya shin wai akwai banbanci tsakanin APC da PDP kuwa domin ko mutanen iri guda ne? Amma Alhaji Sule Lamido gwamnan jihar Jigawa ya ce shi kam da PDP zama dam wai an kai tsoho yayi. To sai dai 'yan Najeriya na cewa irin su Sule Lamido guda nawa ne a faggen siyasar Najeriya?

Sai dai marigayi shugaba Umar Yar'adua ya ce su shugabannin 'yan siyasa sai su zauna su shirya barna mummuna a yi lissafin nawa za'a ba ma'aikacin zabe da 'yansanda da dai wasu domin a shirya rashin gaskiya. 'Yan siyasa su shirya da jami'an tsaro a biyasu domin su kawar da kai idan ana yin magudi. Ya ce wannan ba gaskiya ba ne. Haka ma ana shirya kudi nawa za'a ba masu tsaron akwatin jam'iyyar hamaya domin su ci amanar jam'iyyarsu. Ya ce barnar da ake tafkawa lokacin zabe abun kunya ne domin an yi watsi da gaskiya da akida.

XS
SM
MD
LG