Accessibility links

A cigaba da yiwa 'ya'yanta ragista jam'iyyar APC ta gamu da nasara da kuma matsaloli a Bauchi da Gombe

Rahotanni na nu cewa aikin rajistan da jam'iyyar APC ke yi a duk fadin Najeriya ya samu nasarori da kuma matsaloli.

Injiniya Abubakar Abdullahi shi ne wanda jam'iyyar APC ta tura zuwa jihar Bauchi domin ya shugabanci kwamitin yin rajistan. Ya ce sun samu matsalar wasu kayan aiki wanda ya sa dole suka tafi Jos da Kano kafin su samu wasu dalili ke nan ranaku biyu na farkon soma rajistan sun tafiyar hawainiya. Amma daga bisani ayyuka sun cigaba ba tare da wata matsala ba.

Amma a jihar Gombe dan majalisar wakilai Ahmed Maitantarki ya ce an yi aikin yin ragistan ba bisa kaida ba. Ya ce an yi abubuwa da yawa da basu kan kaida. Kafin a fara yin rajista ya ce su mika kukansu ga uwar jam'iyya domin tsarin da aka tanada bai zo daidai da abun da jam'iyyar ta tsayar ba. Ya ce kaidar da aka yi anfani da shi basu yadda da shi ba. Ya ce sun yi taro da shugabanninsu daga kananan hukumomi har jiha suna kiran uwar jam'iyya ta yi gyara.

Amma Sanato Gwamni Zanna Boma shugaban kwamitin yin rajistan a jihar Gombe ya ce bashi da masaniya kan korafin da Ahmed Mailantarki ya yi. Ya ce idan akwai koke to zai kaiwa uwar jam'iyyar. Sai dai jogo a jam'iyyar Usman Bayero Nafada ya shawarci masu sha'awar tsayawa takara. Ya ce idan jam'iyya tana da farin jini dole ne a samu 'yan takara da yawa. Sabili da haka bayan an kammala rajista ya kamata a zauna a daidaita.

XS
SM
MD
LG