Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Yi Ma Gwamnoni Bakwai Bita Da Kulli


Alamar jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya

Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa ya ce jam'iyyar PDP mai mulki ta fara masu bita-da-kulli ta wajen cinna masu hukumar EFCC da sauran makirce-makirce.

Daya daga cikin gwamnonin PDP masu ja-in-ja da shugabancin jam’iyyar ta PDP karkashin Shugabancin Alhaji Bamanga Tukur kuma gwamnan Adamawa, Alhaji Murtala Nyako ya ce an fara masu bita-da-kulli mai tsanani.

Da ya ke jawabi ga wani taron mata a jihar, Gwamna Nyako ya yi nuni da kama wasu na hannun damar Gwamna Sule Lamido na jiahr Jigawa da Hukumar Yaki Da Almundahana da Dukiyar Al’umma (EFCC) ta yi wanda ya ce ba wani abu ba ne illa cunen da Gwamnatin PDP ke ma masu adawa da abin da ya kira rashin adalcinta. Amma ya jaddada cewa sam su kam ba su razana ba kuma babu gudu ba ja da baya.

Da wakilinmu na jihar Adamawa Ibrahim AbdulAziz ya tambaye shi ko ba su jin tsoro a yanzu, sai gwamna Nyako ya ce ai tunda bai ji tsoron teku ba babu yadda zai ji tsoron wani mahluki. Ya ce ba wani daga cikinsu da ke jin tsoro.

Hakazalika, wakilin namu ya ruwaito wata mambar kungiyar ta mata na jaddada cewa su na nan daram dam a bayan gwamnonin da ke kokarin kawo sauyi irin su Nyako. Ibrahim ya ce wannan abin ya faru ne adaidai lokacin da wani bangare na gwamnonin Nijeriya ke shirin taro a Sokoto karkashin shugabancin gwamna Rotimi Amaechi na jihar Rivers.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:23 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG