Accessibility links

A wata fira da ya yi da Muryar Amurka Gwamnan Kano ya nemi shugabancin jam'iyyarsa ta PDP ya sake salon yadda yake gudanar da harkokin jam'iyyar.

Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya yi fira da Muryar Amurka a Landan yayin da ya je ganin dalibai 'yan asalin Kano su 500 dake karatu a Ingila inda ya bayyana irin abubuwan dake faruwa a jam'iyyar PDP da suka kai ga darewarta.

An tambayeshi ya yi bayani kan abun da ya haddasa sabani a jam'iyyar har shi da wasu suka kira kansu 'yan sabuwar PDP. Gwamna Kwankwaso ya ce shugabanci ko na gida ko na anguwa ko na jam'iyya ko na kasa yana da alaka da shugaba. Idan aka yi dace aka samu shugaba wanda ya tanadi yanayi na kwarai abubuwa zasu dinga tafiya daidai ba tare da an ji wata hayaniya ba ko wani harjitsi. Amma idan aka yi sabani aka samu shugaban da bai gane ba to kullum za'a dinga jin rigingimu da hayaniya suna tasowa da aukuwar wasu abubuwa da irin wannan shugabancin ya haifar. Ya ce PDP jam'iyya ce da ta fito da farin jini kuma jam'iyya ce da ta kunshi mutane masu dimbin yawa da suka fito daga wurare daban daban. Haka ma ta kunshi mutane masu addinai daban daban.

Dr Kwankwaso ya cigaba da cewa yanzu da tafiya ta yi nisa an kawo wani lokaci da aka samu shugabanci da rashin tsari mai kyau wanda ya haddasa kace-nace. Ya ce su da suke gwamnoni suna ganin akwai abubuwa da yawa dake faruwa da ya kamata a gyara. Ya ce akwai wadanda suke fada a waje da suka shafi harkokin siyasa. Akwai kuma wadanda basu fada a waje amma suna shaidawa shugabannin jam'iyyar. Misalin wadanda suke fada a waje su ne maganar zaben Gwamna Amechi da aka zaba a matsayin shugaban gwamnonin Najeriya da maganar rushe kwamitin zastarwar jam'iyyar a jihar Rivers da na Adamawa da ma abun da ya shafi jihar Kano.

A wani bangare na biyu gwamnan Kano ya ce akwai wasu abubuwa da suka shafi kasa ga baki daya wadanda basa yawan maganarsu sabo da suna son a yi sulhu, a gyara domin kada wasu abokan hamayya su yi masu dariya, musamman yadda ake gudanar da shugabancin kasar Najeriya. Akwai bukatu na shugabannisu sake salo yadda za'a samu tsaro a kasa domin mutane su kwanta lafiya su kuma tashi lafiya. Ya kamata gwamnati ta bude dama mutane su samu ilimi, su samu aikin yi, mutane su samu kwanciyar hankali da natsuwa domin kowa ya yi farin cikin cewa akwai shugabanci na kwarai.

Sani Dauda nada rahoto.

XS
SM
MD
LG