Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Za Ta Gudanar Da Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa Ranar Lahadi


Shugaba Muhammadu Buhari (tsakiya) a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC A Abuja

APC ta jaddada cewa za ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ranar lahadi 29 ga watan nan.

Wata sanarwa daga Felix Morka kakakin jam'iyar ta ce za ta gudanar da taron a ranar lahadi da litinin mai zuwa.

A na ganin APC za ta shiga taron fidda gwanin da kimanin 'yan takara 25.

Dan majalisar gudanarwa na jam'iyyar Dattawa Ali Kumo ya ce ba a tantance 'yan takarar ba tukuna.

Gabanin nan jam'iyyar za ta gudanar da zaben fidda gwani na gwamnoni da 'yan majalisar jiha a ranar alhamis din nan.

Bisa ga bayanin, ranar jumma'a za ta gudanar da na majalisar dattawa sai kuma asabar a gudanar da na 'yan majalisar wakilai.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a na ta bangaren ta musanta labarin da 'yan APC su ka dauka cewa a Lagos za ta yi zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa, ta na mai cewa za ta yi taron a rufeffen dandalin wasa na filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja ranar asabar 28 ga watan nan na mayu.

Da alamun kowacce daga manyan jam'iyyun za ta so ta tsayar da wanda ya fi na 'yar uwar ta tasiri a kudu da arewa.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG