Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama Tsakanin ‘Yan Sandan Jihar Kano Da ‘Yan Kungiyar Shi’a


A kalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu wasu dayawa suka raunata a wata arangama da akayi tsakanin ‘yan kungiyar Shi’a da jami’an ‘yan sandan jihar Kano.

Da missalin karfe 8 na safiyar Litinin Dubban ‘yan kungiyar Shi’a sun fito domin gudanar da zanga zanga, har suka toshe hanyar Kano zuwa Kaduna dai dai kwanar Dawaki zuwa gadar Tamburawa. Suka fara fasawa mutane gilasan mota.

Hakan yasa rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro suka kai dauki don kwantar da tarzoma. A cewar DSP Magaji Musa Majiya, arangama tsakanin rundunar ‘yan sanda da ‘yan kungiyar Shi’ar yayi sanadiyar rayukan mutane 8 ‘yan Shi’a. haka kuma an raunata ‘yan sanda 4 da kama mutane 10.

Yanzu haka dai kura ta lafa domin an bude hanyoyin da aka rufe mutane sun ci gaba da zirga zirgarsu da hada hadar kasuwanci a yankunan.

XS
SM
MD
LG