Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsenal Ta Soma Gasar Premier Da Kafar Dama


Arsenal
Arsenal

Kwalliya ta soma biyan kudin sabulu, a yayin da sabbin cefanen kungiyar Arsenal suka soma haskawa, a daidai lokacin da aka soma fafata gasar Premier ta Ingila.

A yayin da aka soma fafata sabuwar kakar wasanni ta gasar kwallon kafa ta Premier ta Ingila, Arsenal ta soma da lallasa sabuwar shiga, kungiyar Fulham da ci 3-0, a wasan da sabbin sayen ‘yan wasanta suka soma haskawa.

Tsohon dan wasan Chelsea Willian ya ba da gudummuwa a dukkan kwallayen 3 da kungiyar ta zura, a yayin da Gabriel da kungiyar ta saya daga Lille akan kudi fam miliyan 23, ya zura kwallonsa ta farko a Ingila.

Tsohon dan wasan Chelsea Willian, a sabuwar kungiyarsa ta Arsenal
Tsohon dan wasan Chelsea Willian, a sabuwar kungiyarsa ta Arsenal

Arsenal ta shiga wasan ne da karfin gaske, yayin da ita ko Fulham ta yi ta fuskantar matsaloli a bayan ta.

A sauran wasannin bude gasar da aka fafata a yau Assabar, zakarun gasar ta Premier wato Liverpool, ta soma fafutukar kare kambinta ne da yin galaba akan daya daga cikin sabon shiga, wato Leeds United da ci 4-3, Crystal Palace kuma ta doke Southampton da ci 1-0, yayin da West Ham ta sha kashi a hannun Newcastle da ci 2-0.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG