Idan aka kwatanta jawabansa na baya da kuma bana, Putin, bisa dukkan alamu ya nuna sassauci, ya ambaci kasashen yammaci ne kawai lokacinda ya tabo batun "takunkumin, wanda yace saboda ana son a tilasta musu daukar matakai da suka saba burin kasarsu. Mai makon haka, Putin yafi maida hankali a jawabinsa na bana na tsawon sa'a daya da minti 10 kan batutuwan cikin gida kamar shirye shiryen kula da jin dadin jama'a da kuma matsalar koma bayan tattalin arziki da kasar take fuskanta, kamin ya karkato kan harkokin kasashen waje. Shugaba Putin yace, "muna son kawaye," amma ba zamu kyale a takamu ko yin biris da muradunmu ba."
Ahalinda ake ciki kuma, shugaba Vladimir Putin ya fada jiya Alhamis cewa a shirye "Rasha take ta hadakai" da sabuwar gwamnatin shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya kara da cewa yana da "muhimmanci a kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu bisa girmama juna da duka sassa zasu amfana."
Shugaba Putimn ya fadi hakan ne a cikin jawabinsa na shekara shekara kan hali da kasar ta Rasha take ciki.