Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Zata Ci Gaba Da Tallafawa Sojojin Syria


Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin

Rasha ta sha alwashi a yau Alhamis cewa zata ci gaba da tallafa ma sojojin gwamnatin Syria a Aleppo har sai an kawar da abinda ta kira ‘yan ta’adda daga birnin.

Wannan furuci na ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya biyo bayan ganawar da yayi a yau alhamisar da takwaransa na Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, wanda yace jami’an diflomasiyyar biyu sun amince da bukatar dake akwai ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.

Rasha da Turkiyya suna goyon bayan babngarori dabam dabam a rikicin na Syria, inda Rasha take dafawa shugaba Bashar al Assad, ita kuma Turkiyya take goyon bayan ‘yan tawayen da suka shafe shekaru 5 suna kokarin kawar da shi daga kan mulki.

Farmakin da sojojin Syria ke kaiwa a Aleppo, wanda ya hada da hare-hare ta sama daga Rasha, ya janyo damuwa game da tsaron lafiyar fararen hula dake unguwannin gabashin birnin inda ‘yan tawaye suka yi tunga. Syria ta jima tana bayyana mayaka masu adawa da ita a zaman ‘yan ta’adda.

Babban jami’in ayyukan jinkai na MDD, Stephen O’Brien yayi kira ga dukkan kasashen dake da tasirin yin wani abu da su dauki dukkan matakan da zasu iya na kare wadannan fararen hula da kuma hana birni mafi girma na kasar Syria zamowa tamkar makabarta mafi girma a kasar.

XS
SM
MD
LG