Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asirin Wata Farfesa Ya Tonu


Jami'ar George Washington ta Amurka

Jami’ar George Washington ta Amurka tana bincike akan wata Farfesa a sha’anin tarihi, da ake zargin ta amsa cewa ta yi shigar burtu a zaman bakar fata ba bisa ka’ida ba a duk tsawon rayuwar aikin ta.

Jami’ar George Washington ta Amurka tana bincike akan wata Farfesa a sha’anin tarihi, da ake zargin ta amsa cewa ta yi shigar burtu a zaman bakar fata ba bisa ka’ida ba a duk tsawon rayuwar aikin ta.

A wani rubutu da aka wallafa a yanar gizo da ya ja hankalin duniya, mawallafiyar da ta yi ikirarin cewa ita ce Jessica Krug, karamar farfesa a bangaren tarihi, ta rubuta cewa bisa hakikani dai bayahudiya ce daga birnin Kansas.

Mawallafiyar ta yi ikirarin cewa a duk tsawon rayuwar ta na babbar mace, ta labe ne a zaman ita bakar fata ce wanda kuma ba ta da ‘yancin yin haka: da farko ta ce bakar fata ce daga Arewacin Afirka, sa’annan ta ce ita bakar fatar Amurka ce, kana kuma ta yi da’awar ita bakar fata ce daga yankin Caribbean.

To sai dai Krug ba ta amsa bukatar da aka yi na ta yi sharhi a shafin na ta na yanar gizo ba. Haka ma jami’ar ta ki bayar da cikakken bayani, to amma ta wallafa a shafinta na twitter cewa “mu na sane da abin da Jessica Krug ta wallafa, kuma mu na bincike akan lamarin.”

Rubutun da aka wallafa dai ya bayyana matukar nadama akan wannan yaudara da aka bayyana a matsayin babban laifi.

Mawallafiyar ta dora alhakin lamarin da “matsalar tabin hankali” da ke addabar ta tun lokacin kuruciya, kana ta ce sau da yawa tana yin yukurin bayyana wannan yaudara da ta ke yi, “to amma fargabar na fin karfin zuciya ta.”

Tarihin Krug da ke shafin jami’ar George Washington na yanar gizo, ya nuna cewa ta kware ne a bangaren tarihin mulkin mallaka da na bakar fatar Amurka. Akasarin rubuce-rucenta sun fi karkata akan al’adun Afirka da zamansu a kasashen waje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG