Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ASUU Zata Shiga Yajin Aikin Gargadi Na Wata Daya


Kungiyar ASUU

A yayin da dalibai ke ci gaba da neman gwamnati ta biya bukatun malaman jami’o’i, kungiyar malaman jami’o’in ta Najeriya wato ASUU ta cimma matsayar fara yajin aiki kai tsaye domin tilastawa gwamnatin kasar biya mata bukatun ta tare da cika yarjejeniyar da suka kulla tsawon shekaru da suka gabata cikin har da shekara ta 2011.

Kungiyar malaman dai ta ce ta yi dogon nazari a ya yin wani taro da ta yi a daren Lahadi inda majalisar zartarwarta ta cimma matsaya a kan cewa malamai su shiga yajin aikin na tsawon wata daya domin tabbatar da gwamnatin Najeriya ta ba da mahimmancin da ya kamata ga batun biyan bukatun mambobinta .

Rahotanni sun yi nuni da cewa a yayin zaman taron majalisar zartarwar kungiyar, ASUU ta yanke shawarar tsunduma cikin yajin aikin na gargadin ne da zimmar ba gwamnatin kasar kafar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta tare kuma da gargadin cewa muddin gwamnati ta gaza biya mata bukatunta, ASUU dai zata shiga yajin aikin na gama-gari.

Sai dai dalibai sun fara bayyana rashin jin dadin su kan matakin da kungiyar ASUU ta dauka da kuma abin da suka bayyana a matsayin rashin kula daga bangaren gwamnatin kasar da ta ki biyan bukatun malaman.

Tuni dai wasu dalibai a kafar Tuwita suka fara nuna fargaba a game da makomar karatunsu musamman ma wadanda su ke ajin karshe a jami’o’in kimiya da fasaha inda su ke cewa "don ‘ya’yan talakawa sun fi yawa a jami’o’in Najeriya ne ya sa ake şakacı da karatunsu."

A wani bangare kuma, da yammacin ranar Lahadi ne kungiyar daliban Najeriya wato NANS ta yi wa kungiyar ASUU da gwamnatin tarayyar kasar gargadi a kan su warware takardamar da ke tsakaninsu don gujewa yajin aikin malaman jami’o’in.

Sai dai tsohon dan majalisar dattawa, sanata Shehu Sani a shafinsa na Tuwita, ya wallafa cewa daliban Najeriya sun fi sanin kungiyar ASUU don tsabar yajin aikin da ta cika shiga fiye da ayyukan kungiyar daliban ta NANS.

Wata mai suna @firstladyship ta ce kungiyar NANS ta zama wani bangaren siyasar gwamnati inda ta shawarci dalibai da su je su koyi sana’o'in hannu kawai don zasu fi amfana la’akari da yadda ba bu aikin yi bayan kamalla karatu a kasar.

Idan ana iya tunawa kuwa tun da dadewa ne kungiyar ASUU ta lashi takobin cewa za ta shiga yajin aikin gama-gari don abin da ta danganta da nuna halin ko-in-kula kan bukatunsu daga bangaren gwamnatin kasar.

ASUU dai ta ce an shafe sama da shekaru goma gwamnati ba ta yi waiwaye kan tsarin yin nazari da kuma duba yiyuwar inganta rayuwa da albashin mambobinta ta aka ce za’a a rika gudanarwa duk wata uku a kasar ba.

XS
SM
MD
LG