Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Ja Hankalin Gwamnati Kan Yiwuwar Fuskantar Matsalar Karancin Abinci A Najeriya


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar (Facebook/Atiku Abubakar)

Atiku ya ba da shawara ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su kafa rundunar sojoji na musamman da za su samar da tsaro ga manoma domin su samu damar gudanar da ayyukansu.

Biyo bayan gargadi da hukumar abinci da aikin noma (FAO) da sashen kula da abinci na Majalisar Dinkin Duniya suka yi game da yiwuwar samun karancin abinci a musamman a arewacin Najeriya, tshohon mataimakin shugaban Nageriya Alhaji Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar karancin abinci da ake fuskanta a kasar kafin ta ta’azzara.

Atiku Abubakar ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken ‘Bari mu magance matsalar karancin abinci da ke tafe kafin ya zama bala’i’, inda ya bayyana cewa gargadin tamkar mubudin idanu ne ga gwamnatin Najeriya idan ta yi la’akari da cewa arewacin kasar kusan shi ne sashen dake ciyar da kasar wanda idan har aka samu fari hakan zai iya shafar fadin kasar dama wasu sassa da ke yammaci.

Abubakar ya kara da cewa babban matsalar dake haifar da karancin abinci a yanzu ita ce, matsalar tsaro da ke hana manoma da sauran ma’aikatan gona zuwa gona, yana mai ba da shawara ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su kafa rundunar sojoji na musamman da za su samar da tsaro ga manoma domin gudanar da ayyukan su.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya cewa ya kamata gwamnati ta baiwa manoma kwarin gwiwa wajen samar da iri da kuma taken zamani ga manoma don domin kawar da aukuwar karancin abinci da yunwa a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG