Accessibility links

AU Tana Kira Ga Magoya Bayan Gadhafi Su San Annabi Ya Faku

  • Aliyu Imam

Jean Ping na tarayyar Afirka yake magana da namena labarai a Addis Ababa.

Shugaban majalisar gudanarwa na tarayyar Afirka Jean Ping yana kira ga mayaka dake goyon bayan shugaba Gadhafi dasu rungumi kaddara cewa an kada su.

Shugaban majalisar gudanarwa na tarayyar Afirka Jean Ping yana kira ga mayaka dake goyon bayan shugaba Gadhafi dasu rungumi kaddara cewa an kada su.

Mr. Ping wanda yayi magana da manema labarai a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha yayi kira ga Mr. Gadhafi da ya “gane” cewa ‘yan adawa sun kwace mulki,sabo da haka ya dauki matakai na hana kara zubda jinni. Daga nan yayi kira ga dukkan sassan biyu da su daina fada domin an kawo karshen rigimar.

Ranar jumma’a kungiyar kasashen Afirkan taki amincewa da majalisar mulkin wucin gadi ta ‘yan tawayen Libya a matsayin halattaciyar gwamnatin Libya. Yace kungiyar zata marabci ‘yan tawayen Libyan idan suka kafa gwamnati data kunshi kowane wane jinsin kasar.

Mr. Ping yace kalmar ko wane jinsi ba yana nufin sai sun saka Gadhafi cikin gwamnatin ba.

XS
SM
MD
LG