Accessibility links

'Yan Tawayen Libya Sun Baiwa Mahaifar Gadhafi Wa'adi....

  • Aliyu Imam

Hotunan Shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi,da dansa Saif-al-Islam.

Shugaba hukumar mulkin wucin gadi ta yan tawaye, Mustafa Abdel Jalil yace sojojinsa zasu kai sumame Sirte idan sojojin dake biyaya ga Gaddafi basu kamalla shawarwarin yin saranda kan ranar asabar ba.

Hukumomin mulkin wucin gadi ta Libya, sun baiwa sojojin dake biyaya ga Moammar Gaddafi a garin Sirte mahaifar shugaban na Libya, wa’adin kwanaki hudu su bada kai.

Shugaba hukumar mulkin wucin gadi ta yan tawaye, Mustafa Abdel Jalil yace sojojinsa zasu kai sumame Sirte idan sojojin dake biyaya ga Gaddafi basu kamalla shawarwarin yin saranda kan ranar asabar ba.

Sojojin yan tawaye sunce suna tsumayen yin fafatwar karshe domin mamaye birnin Sirte. Tun dai lokacinda mayakan yan tawaye suka mamaye birnin Tripoli a makon jiya, ba’a ga Gaddafi ko kuma yayansa masu tasiri guda biyu ba. Wasu suna tsamanin cewa kila Gaddafi ya boye a kudancin kasar ne.

-

XS
SM
MD
LG