Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aung San Suu Kyi Za Ta Yi Jawabi Kan 'Yan Rohingya


Jagorar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi
Jagorar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi

Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, ta jingine zuwanta babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Amurka, inda ake sa ran za ta yi wani jawabi kan rikicin Rakhine da ya tilastawa dubun dubatar 'yan kabilar Rohingya ficewa daga kasar.

Jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi na shirin gabatar da wani jawabi da ake shaukin a saurara a gobe Talata, kan rikicin jihar Rakhine da ya ja hankalin duniya.

Rikicin ya yi sanadin ficewar ‘yan kabilar Rohingya kusan 400,000 daga gidajensu inda suka nemi mafaka a Bangladesh cikin ‘yan makwannin da suka gabata.

Masu fafutika ‘yan kabilar ta Rohingya, sun kai wani hari a wani ofishin ‘yan sanda a watan Agusta.

Hakan a cewar masu fashin baki da masu ayyukan ba da agaji ya sa dakarun kasar suka yi ta azabtar da ‘yan kabilar inda suka rika kona kauyukansu tare da aikata kisan gilla akan mata da yara da ke tserewa rikicin.

Aung San Suu Kyi, wacce ta sha suka daga kasashen duniya saboda kin maida hankali wajen kawo karshen rikicin, ta soke zuwa babban taron Majalisar Dinkin Duniya domin ta magance rikicin.

Ana sa ran jawabin na Aung San Suu Kyi, wacce ta taba lashe kyuatar Nobel ta zaman lafiya, zai kankama ne da misalin karfe 10 na safe agogon kasar ta Myanmar wanda kafafen yada labaran gwamnati za su watsa kai tsaye.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG