Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Australia Na Tuhumar Matashin Da Ya Yi Yunkurin Kai Hari a Melbourne


Wani lokaci a can baya da 'yan sandan Australia suka kai samame a wani yankin birnin Melbourne
Wani lokaci a can baya da 'yan sandan Australia suka kai samame a wani yankin birnin Melbourne

Hukumomin Australia sun fara tuhumar wani matashi da ake zargi da yunkurin kai hari akan dandazon jama'a a lokacin bukuwan sabuwar shekara.

‘Yan Sandan Australia sun tuhumi wani mutum da yunkurin aikata abin da suka kira mummunan harin ta'adanci a lokacin bikin zagayowar sabuwar shekara a birnin Melbourne.

Hukumar tsaro ta bayyana cewa wanda ake zargi mai shekara 20, da haifuwa dan Australia ne amma dan asalin Somaliya, wanda ya shirya harbin mutane da dama da bindiga mai sarrafa kanta.

Matashin ya yi niyyar kai harin ne a wani dandali da ake taruwa mai suna Federation Square a tsakiyar Melbourne a lokacin bikin sabuwar shekara.

Dandalin na Federation Square na daya daga cikin wuraren da mutane suka fi tururuwar zuwa domin bukuwan kasar.

Ana kyautata zaton cewa matashin wanda ba a bayyana sunansa ba yana nuna goyon bayansa ne ga kungiyar ISIS.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG